<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>552</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Yesu mun kangara,
 Gagara muka yi,
 Tun muna ƙanƙanana
 Zamanmu zaman ƙi.
 Shaiɗan ya magance mu
 Ya raba mu da kai
 Da muka yardar masa
 Ya ɓad da mu sosai.

[V2]
 2) Ya Yesu, muguntarmu
 Yanzu sai daɗuwa
 Kamar ta halaka mu
 Mu ma, har abada
 Mun yiwo gudun tsira,
 Da roƙo,  muka zo
 Da ƙazantaccen ranmu
 Ka wanke shi ƙalau.

[V3]
 3) Sa'annan, ya Ubangiji
 Mu naka sababbi,
 Ka tsare mu ga Mugun,
 Har bi da mu ka yi.
 A kwananmu a gaba
 A hannunka mu ke
 Biyayya har ta kasa
 Ga mu, mu naka ne.</lyrics>
<title>Ya Yesu Mun Kangara LW552</title>
</song>